Ba Mutunci Abinda Tahir Fagge Yayi A Wannan Bidiyo

Babban jarumi a masana’antar kannywood wanda yake fitowa a sigar mutunci wato tahir fagge yan kwana Kin nan wasu bidiyo nashi suna ta yawo a shafikan
Sada zumunta wanda wannan bidiyoyin babu kyan gani domin duk wanda ya gansu babu abinda yake fitowa daga bakinsa sai Allah wadaran naka ya lalace
Girma ya fadi, tsufa tayi gaddama dalilin mutane shine irin abubuwan da yake koda karamin yaro ke yinsu abin kyamata ne bare kuma shi babba wanda ake
Kallo mai hankali da tunani kuma matan da yake yin bidiyon dasu yaran cikinsa ne babu wacce baki haifa ba abin ya daurewa masu kallonsa kai sosai duba da
Yadda suka ga yaci gaba da aikata wadannan abubuwan ba tare da yaji cewa fa hakan yana taba masa mutunci hakan kuskure ne shekarunsa sun wuce haka
Saidai ma abun yaci gaba domin wasu bidiyoyin ma a gidan gala aka dauke shi yana ta tika rawa abunsa harda rawar turawa wacce ake kira da (dubstep) har
Yanzu ma ya zama abun tsokana wajen mutane kowa daura bidiyon yake da kuma abinda kowa yake cewa muna masa fatan Allah ya ganar dashi kodan
Mutunci yaronsa a idon duniya. Daya daga cikin bidiyoyin